For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Yi Kira Ga Buhari Da Ya Dawo Da Farashin Gas Yanda Ya Sameshi A 2015

Kungiyar Marubuta kan Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta yi kira ga Shugaba Buhari da ya dawo da farashin gas na girki yanda ya sameshi a watan Mayu na shekarar 2015.

Shugaban Kungiyar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko ne ya sanar da hakan a hirarsa da jaridar PUNCH a jiya Asabar.

Emmanuel ya ce, babu wani abun murna ga ‘yan Najeriya saboda ‘yar raguwar farashin gas din da aka samu a kwanannan.

Jaridar PUNCH ta gano cewa, farashin gas mai nauyin 12.5kg ya sauko daga N8,800 zuwa N8,400 ko N8,200.

A wasu wuraren kuma ya sauko zuwa N8,000 ko N7,800 a ranar Alhamis da ta gabata.

KU KARANTA: Ministar Kudi Ta Zargi Masu Fasakwauri Da Jawo Tsadar Shinkafa A Nigeria

Farashin gas din dai ya yi tashin gwauron zabi ne da kaso 240% a mai nauyin 12.5kg, inda ya tashi daga N3,000 ya kai har N10,200 a watanni 10 na farkon shekarar 2021.

Wannan lamari ya sa, da yawa daga masu amfani da gas din komawa amfani da gawayi ko itace saboda tsananin tsadar da ya yi.

Manajan Shirye-shirye na Tsare-Tsaren Bunkasa Harkokin Gas na Kasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Dayo Adeshina ya ce, Gwamnatin Tarayya tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cigaba da saukar farashin gas din.

A dai cikin hirar tasa da PUNCH, Shugaban Kungiyar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko ya ce, “tsananin tsadar da gas din yai, ya jawo rufe gidajen yin abinci da kananan shaguna, wanda hakan ya kara marassa aikin yi a Najeriya. Kuma tsananin tsadar gas din ya jawo lalata gandun daji wanda hakan ya nuna irin halin ko in kula da wannan gwamnati ke nunawa wajen shirin magance matsalar dumamar yanayi.”

Comments
Loading...