For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Yi Kira Ga ‘Yan Jigawa Da Su Kula Da Kayayyakin Da Suke Siya

Daga: Abubakar Tahir Hadejia

Shugaban Hukumar Kula da Ingancin Kaya ta Kasa (SON), Reshen Jihar Jigawa Sunday Musa Galadima yayi kira ga al’umma musamman ƴan kasuwa da suke shigo da kayan jabu daga kasashen waje suke sayarwa al’umma da su daina, su kuma guji haduwa da hukumar tasu ta SON.

Sunday ya bayyana cewa da yawa daga cikin ƴan kasuwa suna shigo da kaya marasa kyau wanda hakan kan zama barazana ga rayuwar al’ummarsu.

“Haka kuma ya kamata mutane su rinka lura da abubuwan da suke siya musamman in har ba su ga tambarin SON ko kuma MANCAP a jiki ba,” Inji Sunday Musa Galadima

Haka kuma Sunday Musa Galadima ya bayyana cewa da yawa daga masu wannan dabi’ar marasa kishin kasane wanda basa son cigabanta.

“Babu yadda za a yi wanda yake kishin al’ummarsa ya kawo musu abinda zai jawo musu hadari ga rayuwarsu.”

Sunday Galadima ya kara da cewa suna iya kokarinsu wajen shiga lungu da sako na yankunan kasar nan domin ilimantar da al’umma muhimmanci wannan hukumar.

Sunday Galadima ya bayyana cewa cikin shekara mai kamawa ta 2022 akwai shiri na musamman na wayar da kan al’ummar jihar Jigawa.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu mutane sannu a hankali suna fahimtar aikin hukumar ta su.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu taimaka musu wajen zakulo baragurbi cikin al’umma.

Sannan kuma ya yi kira da cewa al’umma dake yin kayan amfani su rinka zuwa ga hukumar ta SON tana musu rijista domin tabbatar da inganci kayan da suke sarrafawa.

Comments
Loading...