Wani shafin Twitter da ya saba fitar da bayanai kan halin da ake ciki a shirin NPower ya yi kira ga ‘yan Batch A da B da su yi watsi da sakonnin da suke samu a kwanakin nan ana umartar su da su yi wani abu.
Shafin mai suna NPVN INFO (NATIONWIDE) ya wallafa wannan sanarwa a yammacin jiya Asabar, inda ya kara da cewa za a waiwaici wadanda suka ci gajiyar shirin kwananan.
Shafin ya kuma yi kira gare su da suna bibiyar shafukan sa da zumunta na shirin NPower domin samun sahihan labarai game da shirin.
A kwanakin nan ne dai aka samu wata sanarwar da ke umartar ‘yan Batch A da B da su danna wasu lambobi wadanda za ciri naira 30 idan sun danna domin su shiga shirin horaswa da aka shirya musu a watan Fabarairu mai zuwa, cikin jadawalin shirye-shiryen sallamar su.