Shugaban Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Babura na farko, Farfesa Sabo Ibrahim Birnin Kudu ya baiyana aniyarsa ta tabbatar da dora sabuwar jami’ar akan tafarkin cigaba na zamani, domin yin gogayya da sauran takwarorinta.
Farfesa Sabo Ibrahim Birnin Kudu ya baiyana hakan ne a yayinda yake karbar bakuncin al’ummar unguwannin Kukar Dansarki da Gangare dake Birnin Kudu, mahaifarsa, a bisa ziyarar taya murna da bada shawarwari da suka kai masa.

Wakilin TASKAR YANCI Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu ya rawaito, cewa Farfesan ya nuna jin dadin sa da wannan ziyarar taya murna da kuma karfafa gwuiwa da yan unguwar tasu suka kai masa, inda ya lashi takobin yin tafiya tare da kowa domin cimma nasara a ayyukan sa.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban tawagar Mal Dan’asabe Charbus ya bayyana makasudin ziyarar da cewa an shiryata ne domin taya Farfesan murnar samun wannan matsayi, a matsayin sa na daya daga cikin yan unguwarsu da sukai nasara a rayuwa, kana su bayyana masa aniyarsu ta bashi gudummawar addu’o’i da shawarwarin da zasu taimaka masa wajen sauke wannan babban nauyin da Allah ya dora masa.
A nasa jawabin babban limamin masallacin Juma’ah na Sabon Gari a Birnin Kudun Malam Sulaiman Datti nasiha ya yiwa sabon shugaban jami’ar fasahar dake Babura tare da addu’ar Allah yayi riko da hannayensa.
Daga cikin ‘yan unguwar tasu da suka kai wannan ziyara har da Alh. Ibrahim Garba Abdullahi FCNA darakta a ma’aikatar kudi ta jihar Jigawa wanda kuma shine mataimakin jagoran tawagar, da Engr. Ashiru Garba PhD (in view) da Malam Aliyu Umar da Malam Sulaiman Aliyu da Malam Aminu Abubakar da dai sauran jama’a da dama.