A karshen watan Satumba na wannan shekarar ta 2021, yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira Tiriliyan 38.005 in ji Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya, DMO.
Ofishin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na intanet jiya mai taken; ‘DMO ya wallafa adadin bashin da ake bin Najeriya na kwata ta 3 ta shekarar 2021’.
Sanarwar ta ce “kamar yanda yake a tsarin aikinsa, Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya ya wallafa yawan adadin bashin da ake bin Najeriya a dai-dai ranar 30 ga watan Satumba na 2021. Bayanan bashi na kasashen waje da kuma na cikin gida wanda gwamnatin tarayya, jihohi 36 da babban birnin tarayya suka ciyo ya nuna cewa ana bin Najeriya Naira Tiriliyan 38.005 dai-dai da Dala Biliyan 92.626 kawo karshen kwata ta 3 ta shekarar 2021.”
Yawan adadin bashin da ake bin Najeriyar ya karu da Naira Tiriliyan 2.540 cikin watanni uku tsakanin 30 ga watan Yuni na karshen kwata ta 2 zuwa 30 ga watan Satumba, 2021.
Ana wani cigaban kuma, Majalissar Wakilai ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ta kara ciyo bashin Naira Triliyan 2.3 wanda yai dai-dai da Dala Biliyan 5.8 da kuma neman tallafin Dala Miliyan 10.
Wannan sabon bashin za a ciyo shi ne daga Bankin Duniya, Islamic Development Bank, China Exim Bank, Chinese Africa Development Fund, da kuma International Fund for Agricultural Development (IFAD).
A lokacin da Majalissar ke amincewa da bukatar shugaban kasar, ta bukaci shugaban da ya da a gabatar mata da ka’idojin karbar basussukan da kuma tallafin domin bibiyar lamarin.