Majalisar dokokin jihar Jigawa ta ce majalisar kansilolin karamar hukumar Ringim ba su da hurumin tsige shugaban karamar hukumar.
Wannan na zuwa ne bayan da kansilolin suka sanar da tsige shugaban karamar hukumar bisa zarginsa da gudanar da wasu ayyuka ba tare da sanin majalisar ba.
Shi ma mutumin da kansilolin ke cewa sun tsige din yace yana nan daram a kan kujerarsa kasancewar ba su da ikon yin hakan.
Kansilolin dai sun aikawa majalisar dokokin jihar Jigawa wasika game da abin da suka yi, don majalisar ta dauki mataki na gaba, amma majalisar ta shawarci kansilolin su koma baya su bi tsarin doka, saboda a cewar shugaban kwamitin watsa labaran majalisar ba su tura musu wasika takanas zuwa wurinsu ba, illa dai sun saka sunansu cikin jerin wadanda ake sanar da su an dauki matakin.
BBC Hausa