For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ana Tsakiyar Rikici, Shugaban Tunisiya Ya Zabi Mace A Matsayin Firaminista

Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied ya nada Najla Bouden Romdhane, injiniya mai aiki a jami’a wanda ke da kwarewar aiki da Bankin Duniya, a matsayin Firaminista a ranar Laraba kusan watanni biyu bayan ya kwace mafi yawan iko a wani mataki da makiyansa ke kira da juyin mulki.

Romdhane, mace ta farko da ta zama Firaminista a Tunisiya, za ta hau kujerar mulki a daidai lokacin da ake tsakiyar rikici, tare da shakku kan nasarorin dimokradiyyar da aka samu a juyin juya halin 2011 ga kuma matsalolin kudade.

Injiniya mai binciken kasa (geologist), Romdhane ita ce ke da alhakin aiwatar da ayyukan Bankin Duniya a ma’aikatar ilimi ta kasar, sai dai kuma ba ta da kwarewar aikin gwamnati.

Da yake magana a wani faifan bidiyo da aka sa a yanar gizo, Saied ya ce nadin nata ya girmama matsayin matan Tunisiya kuma ya nemi ta ba da shawara kan nadin majalisar ministoci a cikin awanni ko kwanaki masu zuwa “saboda mun yi asarar lokaci mai yawa” in ji shi.

Ya kamata sabuwar gwamnatin ta amsa buƙatun da mutuncin ‘yan Tunisiya a dukkan fannoni, gami da kiwon lafiya, sufuri da ilimi, in ji shi.

Saied ya kori Firaminista na baya, ya kuma dakatar da majalisar kasar tare da kame madafun iko a watan Yulin da ya gabata.

Yana fuskantar matsin lamba na cikin gida da na duniya don ya tabbatar da kafa sabuwar gwamnati.

A makon da ya gabata ya yi watsi da yawancin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar, yana mai cewa zai iya yin mulki da doka irin ta soja, a cikin lokacin gaggawa wanda ba a takamaiman matsayi kan al’amura.

Sabuwar gwamnatin da ake kafawa, za ta yi saurin neman tallafin kuɗi don yin kasafin kudi da biyan bashi, bayan Saied a watan Yuli ya dakatar da tattaunawa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

Galibin jiga-jigan siyasar Tunisiya, ciki har da yawancin jam’iyyu a majalisar da aka dakatar, sun ce suna adawa da karban ikon Saied.

Comments
Loading...