A jiya ne dai Alkalin Alkalai Tanko Muhammad ya ajjiye mukaminsa kusan shekara daya da rabi kafin karewar wa’adinsa saboda matsalar rashin lafiya.
Wa’adin Alkali Tanko dai zai kare ne a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2024, lokacin da zai cika shekaru 70 a duniya.
An gano cewa, Alkali Tanko wanda aka nada a shekarar 2019 na fama da matsalar mantuwa, abun da ke zame masa tarnaki wajen iya gudanar da aikinsa.
An gano cewa, tsohon alkalin alkalan ba zai iya jure rikita-rikitar babbar kotun ba, musamman ma abun da ya shafi bincike.
Sai dai kuma, bay a son wasu su yi amfani da matsalar tasa wajen kwacewa ko kuma juya hukunce-hukuncen Babbar Kotu, wanda ake tunanin hakan zai iya jawo rikici a kasar.
Boren da ‘yan uwansa alkalan Babbar Kotun sukai kan yanda yake gudanar da kotun, wani abu ne da ke nuni da munin halin da tsohon alkalin alkalan ke ciki.
Alkalai 14 na kotun kolin dai sun rubutawa tsohon alkalin alkalan takarda inda sukai korafi kan yanda yake shugabantarsu.
Majiyoyi sun ce, Alkali Tanko Muhammad ya samu shawarar likitoci na “ya tsagaita a hankali” kan aiyukansa.
Bincike ya nuna cewa, tsohon alkalin alkalan ya so ya ajjiye aikin tun watanni takwas da suka gabata, amma bai yi hakan ba, inda ya tsahirta dan kadan.
An gano cewa, tsohon alkalin alkalan ya jinkirta saukarsa ne domin Alkaliya Mary Odili ta yi ritaya, saboda idan ya sauka a wancan lokacin ita ce zata maye gurbinsa kuma ba zata dade ba wa’adinta na aiki zai kare, abin da zai iya jawo matsala a babbar kotun.
Ita dai Alkaliya Mary Odili ta yi ritaya ne a ranar 12 ga watan Mayun da ya gabata, bayan ta cika shekaru 70 a duniya.
Wata majiya da jaridar THE NATION ta samu zarafin tattaunawa da ita, ta ce, “Tun daga lokacin da ya gaji tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnogehn, Alkalin Alkalai Tanko Muhammed ke fama da matsalolin da suka shafi lafiyarsa.
“Girman aikin alkalin alkalai ana ganin shi ya sa shi shiga halin matsalar mantuwa. Duk lokacin da yai zaman tattaunawa da ‘yan uwansa yana manta hukuncin da aka yanke, kuma za a iya ganin bai biyo bayan hukuncin da aiki ba.”
Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Alkali Olukayode Ariwoola mai shekaru 67 kuma mafi girman matsayi cikin jerin alkalan Kotun Kolin Najeriya a matsayin alkalin alkalai na rikon kwarya.
Ariwoola dai shine alkalin alkalai na 22 a jerin alkalin alkalan da akai a Najeriya, kuma yanzu haka yana jiran tabbatarwa daga majalissar dattawa.