For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ana Yin Adawa Domin Cigaba Ne Ba Don Gaba Ba

Adawa a siyasance kalma ce da ke nufin sukar bangaren da ba a tare dashi, ta hanyar bankaɗo gazawarsa da kuma nakasun da ya samu.

Shi kuwa ‘dan adawa’ shine mai bincikowa naƙasun da kuma ta inda aka gaza ya yi amfani da kalmomin da ba na cin zarafi ko taɓa kimar mutumtakar abokan adawar tasa ba.

A cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, dokar ƙasa ta ware wani sashi (39) domin ƴan ƙasa suyi amfani dashi a matsayin madogara ta  tofa abin da ya sawwaƙa a mutumce game da irin wainar da ake toyawa a gwamnati.

Na nazarci yanayi da yadda ake adawa da ma yadda wakilai ko masu riƙe da madafun iko suke kallon adawa a jihata ta Jigawa. Idan na fara da ɓangaren yan adawa sai nake ga kamar ba a fahimtar adawar ana kuma yin watsi ko mantawa da wancan sashi na cikin kundin tsarin mulki da nayi magana akansa a baya. Lokuta da dama sai a zaƙe da yin adawa ta kai ga ana cin zarafi ko taɓa kima, yayin da a wasu lokutan ake kan-tafi da damarmaki masu ɗumbin yawa.

A taƙaice dai akwai buƙatar sake shirin yadda ake adawa a Jigawa da ma wasu jihohinmu na Najeriya da dama.

Ta ɓangaren manya ko kuma na ce masu riƙe da madafun iko (zaɓaɓɓu) kuwa sai kaga ƙarfi da yaji mutum ya rufe ido ya fututtuke shi ala dole yafi ƙarfin ayi masa adawa. Ji yake kamar ya gamsar da kowa da komai, yana ji kamar ya biya kowa ladan ƙuri’arsa, ji yake kamar idan aka yi masa adawa kujerarsa tana rawa. Ka ga an baza koma ta ko ina ana jiran a ji ƙyas ace wane baya son mu, kai kace  ya gama biyan haƙƙin kuri’u da rantsuwar da ya yi da Littafi mai Tsarki.

Mafi kamantuwa dai kowane rantsatstse ya fahimci adawa domin ita adawa a siyasa irin ta demokuraɗiyya gishiri ce tana kara danɗanon siyasa idan aka yi ta dai-dai kima, kuma idan ta yi kaɗan to ɗanɗanon siyasa baya fitowa, haka in ta yi yawa kuwa an ɓata sabgar baki ɗaya.

Ƴan siyasa  su nazarci ma’ana su kuma amfana da yadda ake ADAWA sai ka ga an zauna lafiya kuma al’umma ta amfana, domin ta hanyar amfani da adawa ne za ka ci moriyar tunanin mutane dubbai waɗanda ka zata da wanda baka tsammata ba.

Yar Jarida
Zunnura Ishaq Jibriel

Comments
Loading...