Ana zargin Digacin Ɗan Gulam da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa, Umar Ibrahim da yin fyaɗe da yi wa yarinya mai suna Hannatu Yahaya ciki da kuma sanya mata cutar ƙanjamau.
Wannan na ƙunshe ne a wasiƙar da Babban Mai Shigar da Ƙara na Jihar Jigawa a Ma’aikatar Shari’a, Kabiru Abdullahi Esq., ya aike wa Sakataren Majalissar Masarautar Dutse mai ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Oktoba, 2023.
Wasiƙar na ɗauke da taken ‘Sanar da kama Umar Ibrahim (Digacin Dan Gulam) bisa laifin yin fyaɗe wanda ya saɓa da Sashi na 3 (1) (A da D) na Kudin Dokar Hana Laifukan Cin Zarafin Mutane, VAPP ta shekarar 2021’.
To sai dai kuma digacin ya musanta zargin da ake masa a tattaunawarsa da wakilin jaridar DAILY TRUST.
Rahotanni sun nuna cewar, akwai matsin lamba a kan masarauta na ta binne maganar duk da shigar gwamnatin jihar ta ofishin Babban Lauyan Gwamnatin jihar.
A wasiƙar an nuna cewar, digacin ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Shari’a ta Gwaram, yana zargin yarinyar, mahaifinta da wani mai suna Sule Umar ɗan garin Dan Gulam da ɓata masa suna.
To sai dai kuma binciken da Sashin Binciken Manyan Laifuka na Shelkwatar Ƴansandan Jihar Jigawa ya tabbatar da laifukan haɗinbaki wajen aikata babban laifi da kuma yin fyaɗe a kan Umar Ibrahim.
Wasiƙar ta ce, Babban Lauyan Gwamnati na Jigawa ne ya bayar da umarnin a rubuta ta domin sanar da Mai Martaba Sarki ƙorafin fyaɗe da sanya ƙajamau da wani mai suna Ya’u Muhammad ya shigar, inda yake zargin Umar Ibrahim (Digacin Dan Malam) da yi wa ƴarsa fyaɗe wanda ya sa ta samu ciki ta kuma kamu da ciwon ƙanjamau.
A wani ɓangaren kuma, iyalan yarinyar da abun ya shafa, na buƙatar ƙungiyoyin ci gaban al’umma da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da su shiga maganar domin tabbatar da an yi adalci gwargwadon tanadin dokar VAPP ta shekarar 2021 ta Jihar Jigawa.