Dan Takarar Gwamna a zaben da aka gabatar ranar Asabar da Talatar da ta gabata a jihar Anambra daga jam’iyyar APC, Sanata Andy Uba, ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan da aka sanar jiya.
Andy Uba ya bayyana a sanarwar da akaiwa take da ‘Sanata Andy Uba ya yi Watsi da Sakamakon Zaben Gwamna na Anambra’ sanarwar da mai magana da yawun yakin neman zabensa, Jerry Ugokwe ya fitar a yau Alhamis.
Ya bayyana sakamakon zaben da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa ta fitar a matsayin na bogi wanda bai dace da fata da kuma abin da mutanen jihar suka zaba ba.
Sanarwar ta ce, “sanannen dan takararmu, Sanata Andy Uba ya gamu da halin magudi da kunbiya-kunbiya daga Hukumar Zabe hadin guiwa da mulkin Willie Obiano da kuma jami’an tsaron da aka tura domin kula da zaben gwamnan a jihar Anambra.
“Rashin gaskiya ya mamaye zaben, wulakanci da takurawa masu zabe don kawai a budawa jam’iyyar APGA hanya ta ci zabe.
“Alal misali, a rumfunan zaben da na’urar tantance masu zabe ta ki aiki, Hukumar Zabe kawai ta cigaba da yin zabe. Akwai gurare da yawa inda hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben da ya haura adadin wadanda aka tantance a gurin.
“Wani abu da zai kara tabbatar da haduwar gwamnatin Obiano da Hukumar Zabe shine bayyana sakamakon zabe a kafafen sada zumunta na jam’iyyar APGA kafin a samu sanarwa daga Hukumar Zabe. Abin mamaki shine, dukkan kuri’un da jam’iyyar APGA ta sanar sun zo dai-dai da wadanda Hukumar Zabe ta sanar daga baya.
“Abu ne da ba zai taba yiwuwa ba a ce, dan takararmu da ya sami kuri’u sama da 200,000 a zaben fidda gwani na APC a ce an ba shi kuri’u 43,000 da kadan daga Hukumar Zabe.
“Abin mamakine a ce APGA da kusan kaso 80 cikin 100 na ‘ya’yanta suka sauya sheka zuwa APC kafin zabe a ce ta lashe zabe. Mataimakin Gwamna mai ci, ‘yan majalissun tarayya guda bakwai, ‘yan majalissun jiha guda goma, dan kwamitin amintattu na APGA, masu baiwa gwamna shawara da mataimaka na musamman da dama, hadi da sanata mai ci dan jam’iyyar PDP duk su dawo APC kafin zabe, amma duk da haka a ce APGA ce tai nasara. Wannan ba karamin abun dariya ba ne.”
Kungiyar yakin neman zaben Andy Uba ta ce za ta kwato ‘yancinta da aka sace mata iya karfinta kamar yanda shari’a ta bayar da dama.