Fitar da danyen mai a Najeriya ya yiwo kasa zuwa ganga 972,000 a duk rana a tsawon kwanakin watan Agustan 2022, yayin da kasashen Angola da Libya suka wuce Najeriya ta yanda kowaccensu ke fitar da wanda ya haura adadin na Najeriya a watan da ake magana a kai, in ji Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC.
Kungiyar OPEC ta bayyana hakan ne a rahotonta na watan Satumba, inda ta tabbatar da alkaluman da Najeriya ta fitar a kan lamarin.
A makon da ya gabata, kafafen yada labarai sun rawaito cewa, danyen man da Najeriya ke fitarwa ya fado kasa da ganga miliyan daya a watan Agusta na shekarar da muke ciki, fado mafi kasa cikin shekaru da dama da suka gabata.
Rahoton na OPEC ya nuna cewa, fitar da danyen mai a Najeriya ya yiwo kasa a watan Agusta, 2022, inda ya fado kasa da ganga miliyan daya a duk rana zuwa ganga 972,394 a kowacce rana.
Alkaluma daga bangaren gwamnatin Najeriya sun nuna cewa, fitar da danyen mai a kasar, ya fado daga ganga 1,083,899 a kowacce rana a watan Yuli zuwa ganga 972,394 a kowacce rana.
Da take tabbatar da wadannan alkaluma a rahotonta na Satumba, 2022 a jiya Talata, OPEC ta bayyana cewa, fadowar fitar da danyen mai a Najeriya ya sanya kasashen Angola da Libya sun kere ta a fitar da danyen man a watan da ake magana a kai.
Rahoton ya ce, Angola ce kasa mafi fitar da danyen mai a Afirka a watan Agusta, 2022 inda take fitar da akalla ganga miliyan 1.187 a kowacce rana.
Rahoton ya kuma ce, fitar da danyen man a kasar Libya na tsakanin ganga miliyan 1.123 a kowacce rana ta watan na Agusta, abun da ya sa ta zo na biyu a Afirka a yawan fitar da danyen mai.
Rahoton ya kara da cewa, fitar da danyen mai ya karu a musamman kasashen Libya da Saudi Arabia, yayin da kuma ya sauka a Najeriya.