Daga: Ahmed Ilallah
Ba sai an yi maganar waye ne Farouk ba, in ana maganar jamaíyar APC a Nijeriya, Farouk Adamu Aliyu sune farkon shu’hada’un Shugaba Muhammadu Buhari tun da ga jamaíyyar APP, ANPP, CPC da ma ita kanta APCn.
Ba kawai a dandalin siyasar JIgawa ba kadai, a fadin Nijeriya ma, ya shahara a lokacin da ya fara zama Dan-Majalissa na farko da aka fara kada masa kuri’ar kiranye, lokacin da yake wakiltar Buji da Birnin Kudu a Majalissar Tarayyar Nijeriya, yin nasararsa a tsakiyar lokacin da suke rigima da gwamnansa Saminu Turaki, wannan ja’injar ta fito da shi a fagen siyasar Nijeriya.
Farouk Adamu, ana ganin kamar babu na biyun sa a kusanci da Shugaba Buhari, hatta kujerar da Buhari yake kai, Fafouk Adamu Aliyu ne ya jagoranci sayawa Buhari Form din da yayi takara a 2019. Ku san babu wani abu da ya shafi APC da baza ka ga Farouk Adamu ba a ciki dumu-dumu ba. A lokacin da Buhari yayi takara a jama’iyar CPC, Farouk Adamu ne yayi masa takarar gwamna a Jigawa. Tun shigar Buhari siyasa babu wani juyi da yunkuri da Buhari zai yi a siyasa ba tare da Farouk Adamu ba.
Ko, a lokacin da aka kafa APC a Jigawa, jagororin da suka jagoranci kafa Maja (APC), wato Badaru Abubakar (Chairman), Ibrahim Hassan Hadejia (Secretary) da Farouk Adamu Aliyu (Treasurer) ne suka jagoranci kafa ta a Jigawa, a cikinsu ukun nan, Farouk ne ba muga wani mataki da ya taka ba, Badaru ya zama gwamnan Jigawa har sau biyu, Ibrahim Hadejia yayi Mataimakin Gwamna, a yau ma shine Sanata, amma har yanzu ba mu san makomar Farouk ba.
Hatta a tsaka mai wuyar da jamaíyar APC ta shiga kafin a kai ga zabar shugabannin jama’iyar da akayi a wannan watan, Farouk Adamu na kan gaba wajen warware rigimar jama’iyar, don ya na daga cikin jagororin da suka je London wajen Buhari yayin da yake zaman jinya, don warware matsalar shugabancin rikon jama’iyar tsakanin gwamnan Yobe da na Niger.
Wai shin menene makomar Farouk Adamu Aliyu ne a APCn yau? Bayan a karo na biyu ya gaza samun goyon bayan jagororin jama’iyar APC, musamman gwamnonin APC na amince masa ya zama mataimakin shugaban jama’iyar na Arewa a karo na biyu, wanda a baya ma ya samu tasgro a kan neman kujerar?
Duk da a wannan karon, an ce yana daga cikin mutane biyar da aka ce suna cikin zabin Buhari wajen yin yarjejeniyar shugabancin, amma sai ga shi a wannan karon ma an yi masa tutsu.
Duk da cewa baza ace Buhari da APC suna son kammala lokacin su ba tare da sakawa irin Farouk ba a siyasance, ganin yadda nasa suke cikin, musamman ma a jihar Jigawa da ganin yadda ya bunkasa ta fannin tattalin arziki, wanda a yanzu a na ganin gonarsa ta zamani ALU Farms babu kamar ta ba, tutar Nijeriyar da ke cikin gonar babu kamar ta a fadin kasar nan, wannan alamu ne na cewa a na damawa da shi a gwamnatin.
Shin kuwa APC da Buhari sun yi wa irin su Farouk adalci, in har suka musu tutsu a irin wannan lokacin, bayan daukar tsawon lokaci na kasancewa shu’hada’u da ganin nasarar jamaíyar da shugabaninta?
Dukda cewa baza a ce komai ya zo karshe a tafiyar APC karkashin jagorancin Buhari ba, zama a iya cewa yanzu ma a ka fara, domin a kwai fidda yan takarkarun da zasu shiga kakar zaben 2023, shin ko shine zai gaji Badarun? Lokaci kadai dai muke jira.
alhajilallah@gmail.com