Daga: BBC Hausa
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma babbar jam`iyyar hamayyar kasar, wato PDP sun bayyana rashin goyon bayansu a siyasance kan gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar `yar tinƙe ko ƙato-bayan-ƙato.
A ranar Talata ne `yan majalisar dokokin ƙasar suka zartar da kudurin dokar da zai tilasta wa jam`iyyun siyasa gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar `yar tinƙe.
Sai dai a wata ganawa da manema labara, shugaban ƙungiyar gwamnoni na Jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya yi fatali da zaɓe ta hanyar ƴar tinƙe, yana mai cewa yin hakan zai sa aiki “ya yi wa hukumar zaɓe ta INEC yawa.”
A cewarsa, matakin ba shi da gurbi a shari’ance kuma yana cike da kalubale.
Gwamna Bagudu ya ce ya kamata a samu wani zaɓin bayan zaɓen ‘yar tinƙe ta yadda jam’iyyu za su yi aiki da salon da ya kwanta musu a rai.
A nata ɓangaren, jam’iyyar PDP ta bakin sakatarenta na ƙasa, Sanata Ibrahim Umar Tsauri, ta ce ba ta ga wani alheri tattare da tanadin da dokar zaɓen ta yi na tilasta wa jam`iyyun siyasa bin tsarin `yar tinƙe wajen gudanar da zaɓen fid da gwani ba, musamman ma a zaɓen `yan majalisun dokokin ba, face dora wa `yan majalisar ɗawainiyar da babu gaira ba sabar.
Jam`iyyar ta yi zargin cewa matsalar wasu ce take nema ta shafi `ya`yanta, tana zargin cewa akwai gwamnonin wasu jihohi na wasu jam`iyyu masu halin kama-karya, waɗanda suke tanƙwara wakilan jam`iyya a zaɓen fid da gwani, waɗanda aka yi gyaran fuska ga dokar zaɓen da nufin taka musu birki, alhali ba ta da irin wannan matsalar a tsakanin gwamnonin da ke rike da tutocinta.
Jam`iyyar PDPn ta ce za ta jira ta gani ko shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai sanya hannu a kan dokar kafin ta dauki mataki.