Bayan debe lokaci ana dakon sakamakon rikicin cikin gida na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Kwamitin Rikon Jam’iyyar na Kasa karkashin Mai Mala Buni ya fitar da tsarin samar da daidaito a mulkin jam’iyyar na jihar.
A yau Litinin ne kwamitin ya saki wata takarda mai dauke da sa hannun Abdullahi Y Gashua, Shugaban Ma’aikatan Shugaban Jam’iyyar na Kasa wadda ta baiyana tsarin da za a bi domin samun daidaito.
Takardar ba ta baiyana karara tsagin da zai karbi shugabancin jam’iyyar ba, ko kuma ambata sunan wani a matsayin shugaba ba, sai dai ta kardar ta jaddada matsayin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin jagoran jam’iyyar na jihar, inda ta bukace shi da yai adalci a jagorancinsa.
Sanarwar ta zo da tsarin samar kananan kwamitoci da ta kira caucus wanda aka dorawa nauyin fito da shugabancin jam’iyyar a mazabu da matakin kananan hukumomi.
Mambobin caucus din sun hada da: Dan Majalissar Dattawa idan ya fito daga karamar hukumar, Dan Majalissar Wakilai idan ya fito daga karamar hukumar, Dan Majalissar Jiha idan ya fito daga karamar hukumar da shugaban karamar hukuma mai ci da mataimakinsa.
Sauran sune, Kwamishina idan akwai a karamar hukumar, Mai Ba da Shawara na Musamman idan akwai a karamar hukumar, mamba na Kwamitin Riko na Jam’iyyar na Kasa idan akwai a karamar hukumar, Minista idan akwai a karamar hukumar da kuma mace daya wadda Gwamna Ganduje zai nada da shawarar tsohon Gwamna Shekarau.
Wadannan kwamitoci za su fitar da tsarin jagoranci bisa bin tsarin raba dai-dai tsakanin bangarori biyu masu sabani da juna, tare da mika rahoton su ga babban kwamiti na jiha hadin guiwa da kasa domin tantancewa da kuma amincewa.
Wannan babban kwamiti yana da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau a ciki.
Sauran yan kwamitin sune, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Yakubu Dogara, Sanata Abba Ali da kuma sakatariyar jam’iyyar.
Gwamna Ganduje shine wanda zai jagoranci wannan babban kwamiti inda tsohon Gwamna Shekarau zai zame masa mataimaki.
Haka kuma kwamitin zai zauna a Kano ya yi aikinsa tare da gabatar da rahoto ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.