For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Mika Wa Yankin Arewa Muƙamin Shugabancin Jam’iyyar – El-Rufai

Gwamnonin APC sun gana da Buhari ranar Talata game da babban taron jam’iyyar na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ware wa yankin arewacin ƙasar muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023.

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya faɗa wa manema labarai, jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata, cewa jam’iyyar ta amince ta rarraba muƙaman da babu kowa a kai a Kwamatin Ƙoli na jam’iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta na ƙasa.

Hakan na nufin muƙamin shugabancin wanda John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole suka riƙe a baya, dukkansu ‘yan Kudu, zai koma Arewa.

“Mun amince da wani tsari na karkasa muƙamai ga dukkan shiyyoyin siyasa. Shiyyoyin Arewa za su samu muƙaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka,” a cewar Gwamna El-Rufai.

Yayin taron, gwamnonin jam’iyyar ta APC sun amince da sabon lokacin da jam’iyyar ta zaɓa don gudanar da babban taronta na ƙasa duk da cewa an samu rabuwar kai tsakaninsu.

Gwamna El-Rufai ya ce ba zai yiwu a tara gwamnoni har 22 ba “kuma a ce ba a samu bambancin ra’ayi ba”.

Ranar Litinin ne kwamatin riƙo na shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa ya fasa gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Fabarairu sannan ya mayar da shi 28 ga Maris.

“An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwamnonin APC game da lokacin taron,” in ji El-Rufai kamar yadda mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Tolu Ogunlesi ya ruwaito shi yana faɗa.

Ya ƙara da cewa: “Wannan kuma wai shi ‘yan jarida ke kira gwamnoni marasa haɗin kai. Babu yadda za a yi a tara gwamnoni 22 kuma kowa ya amince da kowane irin ƙudiri. Za a iya samun bambanci amma idan aka kira shi rabuwar kai to an wuce gona da iri.”

Baya ga sabuwar ranar gudanar da babban taron, APC ta shaida wa hukumar zaɓe ta INEC cewa za ta fara gudanar da taron na shiyya-shiyya tukunna daga ranar 6 ga watan Maris, inda za a zaɓi shugabanni a matakin shiyya.

Magana Da Murya Ɗaya

Jim kaɗan bayan ganawar da suka yi da Buhari, Gwamna El-Rufai ya ce gwamnonin sun amince da wani tsari “na adalci” ga kowane sashen siyasa na Najeriya.

“Bayan ganawarmu da shugaban ƙasa a yau (Talata), mun haɗu a kan abu ɗaya. Mun amince da wani tsari mai adalci da kuma ingantacciyar hanyar rarraba muƙamai ga dukkan sashen siyasa,” a cewarsa.

“Cikin ikon Allah nan da 26 ga watan Maris za mu gudanar da babban taro na ƙasa.

“Babu wata tantama cewa kan gwamnonin APC a haɗe yake wajen yunƙurinmu na tabbatar da cewa ‘Peoples Destruction Party’ ba ta dawo kan mulki ba.”

(BBC Hausa)

Comments
Loading...