Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewar Babban Taronta na Kasa zai kasance ranar 26 ga watan Fabarairu mai zuwa.
Wannan ya tabbata ne bayan shugabancin jam’iyyar ya amince da jadawalin yanda za a gudanar da aiyukan da suka jibinci Babban Taron wanda zai zo nan da kasa ta sati shida.
A wani jawabi da mai magana da yawun jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe ya a ranar Laraba, ya bayyana cewa, amincewa da jadawalin, ya biyo bayan amincewa da Kwamitin Riko na jam’iyyar yai a zamansa na 19 a ofishin jam’iyyar na kasa da ke Abuja.
KU KARANTA: Shugaban APC Zai Fito Daga Arewa Ta Tsakiya Yayinda Sakatare Zai Fito Daga Kudu Maso Gabas
Akpanudoedehe ya kuma ce, babu wani lokaci da aka tattauna batun mika shugabanci zuwa wani yanki kafin Babban Taron.
“Na zo nan ne domin na musa labaran kanzon kurege da ke zagayawa a kafafen sa da zumunta na cewa mun mika shugabanci zuwa wani yanki. Har yanzu ba mu yanke hukunci a kan yankin da shugabanci zai fito ba.
“Labarai da kuma raderadin da ke zagaya, ba gaskiya ba ne. Ba mu tattauna hakan ba a zaman mu. Ya kamata mutane su yi watsi da labarin, saboda labarin kanzon kurege ne, ba gaskiya ba ce.”