For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Rantsar Da Shugabannin Jam’iyyar Na Jihohi 34 Banda Na Jihohi 2

A shirye-shiryen gudanar da Babban Taronta na Kasa a ranar 26 ga Fabarairu, 2022, Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC ta rantsar da shugabannin jam’iyyar reshen jihohi 34 tare da Birnin Tarayya, Abuja.

Jihohi 2 da ba a rantsar da shugabanninsu ba sune Kano da Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.

An gudanar da taron rantsuwar yau Alhamis a Abuja.

Hukuncin dakatar da rantsar da shugabannin jihohi biyun ba ya rasa nasaba da rikice-rikicen da suka ki ci suka ki cinyewa a jihohin.

Sunayen wadanda aka rantsar ranar Alhamis din wanda PlatinumPost ta saki sun hada da; Dr. Kingsley Ononogbu (Abia), Alh Ibrahim Bilal (Adamawa), Mr Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom), Hon Basil Ejike (Anambra), Alh Babayo Aliyu Misau (Bauchi), Dr. Dennis Otiotio (Bayelsa), Mr Augustine Agada (Benue), Hon. Ali Bukar Dalori (Borno), da Mr. Alphonsus Orgar Eba Esq. (Cross River).

KU KARANTA: Jadawalin Gudanar Da Babban Taron APC Na 2022

Sauran sune Elder Omeni Sabotie(Delta), Hon. Stanley Okoro Emegha (Ebonyi), Col David Imuse mai ritaya (Edo), Barr. Omotosho Paul Ayodele (Ekiti), Chief Ogochukwu Agballah (Enugu), Mr Nitte K Amangal (Gombe), Dr Macdonald Ebere (Imo), Hon. Aminu Sani Gumel (Jigawa), Air Cdre Emmanuel Jekada (Rtd) (Kaduna), Alh. Muhammed Sani (Katsina), Alh. Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) da Hon. Abdullahi Bello (Kogi).

Sunayen sun kuma hada da Prince Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara), Hon. Cornelius Ojelabi (Lagos), Mr John D Mamman (Nasarawa), Hon. Haliru Zakari Jikantoro (Niger), Chief Yemi Sanusi (Ogun), Engr Ade Adetimehin (Ondo), Prince Adegboyega Famodun (Osun), Hon Isaac Omodewu (Oyo), Hon Rufus Bature (Plateau), Chief Emeka Bekee (Rivers). Hon Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba), Alh Muhammed A. Gadaka (Yobe), Alh. Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da kuma Alh. Abdulmalik Usman (FCT).

Comments
Loading...