For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Sa Ranar 25 Ga Fabarairu Domin Zaben Shugabaninta Na Kasa

Kwamitin Shugabancin Riko na Jam’iyyar APC, karkashi Gwamna Mai Mala Buni ya sanya 25 ga watan Fabarairu na shekarar 2022 a matsayin ranar da za a gudanar da Babban Taron Jam’iyyar na Kasa domin zaben shugabannin jam’iyyar a matakin kasa.

Sanya ranar ya biyo bayan matsain lamba da Gwamna Buni yake samu daga gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Wannan sabon hukunci kan ranar gudanar da Babban Taron Jam’iyyar ba tabbatacce ba ne, kasancewar har sai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar da kuma mambobin Kungiyar Gwamnonin APC sun amince da shi.

Wata majiya da PUNCH ta samu zantawa da ita, ta sanar da cewa, “an ce mana kwamatin riko ya zabi 25 ga Fabarairu saboda matsin lamba da akai musu. Duk da haka wannan rana ba tabbatacciya ba ce, za a iya canja ta a kowanne lokaci.”

KU KARANTA: An Dage Zaben Shugabannin APC Na Kasa Daga Watan Fabarairu

Wata majiyar kuma da jaridar BLUEPRINT ta samu, ta bukaci boye a sunanta, inda ta ce, “ina tabbatar maka da cewa, Babban Taronmu zai gudana ranar 25 ga Fabarairu a nan Abuja. Wannan tabbas ne daga wajen kwamitin riko.

“Kwamitin da Buni yake jagoranta ba yana kalubalantar wadanda suke son a yi Babban Taron a Fabarairu ba ne, sai dai kwamatin yana so ne a samu yanayi ne wanda ba zai kawo rabuwar kai da yawa ba a Babban Taron.

“Idan har ba a magance matsalolin da suke addabar jam’iyyar ba, za su kara dagula jam’iyyar har ma bayan Babban Taron, kuma ka tuna fa bayan wannan Babban Taro za mu fuskanci zabe na kasa,” in ji majiyar.

Mai Mala Buni dai ya shiga cikin matsin lamba ne daga gwamnoni da dama a satin nan, wadanda suka zarge shi da wasu mutane biyu da kokarin lakume jam’iyyar.

Sun kuma zarge shi da yunkurin neman takarar mataimakin shugaban kasa, inda yake shirye-shiryen cusa yaransa a jam’iyyar ta hanyar kirkirar tsarin sasanto.

Comments
Loading...