For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Samu Karuwar ‘Yan Majalissu 11 Daga PDP Da APGA

Shugaban kwamitin riko na shirya zababbukan All Progressives Congress (APC), Gwamna Mai Mala Buni, ya karbi ‘yan majalissu 11 ‘yan jihar Anambara wadanda suka shiga jam’iyyarsa daga jam’iyyun All Progressives Grand Alliance (APGA) da Peoples Democratic Party (PDP).

Daraktan yada labarai na kwamitin Buni, Mamman Muhammad ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Alhamis din nan.

Ya ce ‘yan majalissun sun hada da ‘yan majalissar tarayya masu ci guda 5, da tsoffi guda 4 da kuma ‘yan majalissar jihar guda 2.

Sun hada da Douglas Egbuna, Ebuchi Offor, Vincent Oguwelu, Ifeanyichukwu Ibezi, Emeka Anoku, Chris Emeka da Ifeanyi Monah.

Sauran sune, Ohwudili Ezenwa, Chinwe Nwaebili,.Chuma Nzeribe da Emeka Azubogu.

Mamman ya ce, Mai Mala Buni, wanda kuma shine gwamnan jihar Yobe, ya taya sabin mambobin murna, inda y ace sun yi zabi mai kyau da suka shiga jam’iyyar APC da kuma jawo jama’arsu zuwa cikin tafiyar al’ummar kasa.

“Kun yi kyakkywan zabi alokacin da ya dace, za ku more duk wani hakki da kuma damar da ake samu a jam’iyya” In ji Buni a cikin sanarwar.

Sabbin ‘yan jam’iyyar sun yabawa Buni, bisa aiwatar da jagorancin da ake da kuma ciyar da jam’iyyar gaba.

Sun kuma yi alkawarin kawo mazabunsu ga jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa, wanda za a gudanar ranar 6 ga watan Nuwamba.

Mammam ya kara da cewa, Shugaban Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Ovie Omo-Agege, Gwamnonin jihohin Imo, Kogi, Kano, Jigawa da Kebbi ne suka temakawa Mai Mala Buni wajen karbar sabbin ‘yan jam’iyyar a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Abuja.

(NAN)

Comments
Loading...