For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Sanar Da Sunan Sanata Ahmad Lawan A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Maslaha

Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar da sunan Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na maslaha na jam’iyyar.

Abdullahi Adamu ya yi wannan sanarwar ne a zaman shugabannin jam’iyyar na ƙasa a yau Litinin a Abuja.

Ya ce ya sanar da wannan matsaya ne bayan ya tuntubi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Wannan matsaya dai ta saɓa da buƙatar gwamnonin APC goma sha ɗaya na yankin Arewa, da suka buƙaci cewa takara ta koma yankin Kudu bayan ƙarewar wa’adin Shugaba Buhari na shekara 8.

An dai rawaito cewa, a farkon wannan rana, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin APC na yankin Arewa a fadarsa da ke Abuja.

Wannan dai na zuwa ne, a tsaka da shirye-shiryen fara babban taron jam’iyyar APC, domin zaɓar wanda zai mata takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen shekarar 2023.

Comments
Loading...