Jam’iyyar APC ta saki jadawalin yanda za ta fuskanci zabubbukan cike gurbi a jihohin Cross River, Imo, Ondo, da Plateau kamar yanda Dokar Zabe ta 2010 ta tanada da kuma bin tsarin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC.
Jadawalin da APC ta samar wajen tunkarar zabubbukan cike gurbin mazabun majalissun, Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe ne ya sanya masa hannu.
Zabubbukan cike gurbin za a yi su ne a Mazabar Dan Majalissar Tarayya ta Arewacin Akure/Kudancin Akure a jihar Ondo; Mazabar Dan Majalissar Tarayya ta Arewacin Jos/Bassa a jihar Plateau; da kuma Mazabar Dan Majalissar Jiha ta Pankshin ta Kudu a Plateau.
Sauran sune, Mazabar Dan Majalissar Tarayya ta Ogoja/Yala a jihar Cross River; Mazabar Dan Majalissar Jiha ta Akpabuyo a jihar Cross River; da kuma Mazabar Dan Majalissar Jiha ta Ngor-Okpala a jihar Imo.
KU KARANTA: Hukumar Zabe Ta Sanya 26 Ga Fabarairu Domin Zabubbukan Maye Gurbi
Jam’iyyar APC ta kasa ta tura jadawalin shiryawa zaben ga ressanta na jihohin a ranar Talata.
Jadawalin ya nuna cewa, za a fara siyar da takardar neman takarar a jiya Talata, yayinda aka sanya ranar 24 ga Janairu a matsayin ranar karshe ta karbar takardun da aka cike.
Za a tantance ‘yan takarkarun jam’iyyar APC domin zabubbukan cike gurbin a ranar 26 ga watan Janairu inda kuma za a bayyana korafe-korafe kan tantancewar a ranar 28 ga watan Janairu, 2022.
Za a gudanar da zaben fidda gwanayen jam’iyyar APC domin zabubbukan a ranar 1 ga watan Fabarairu, 2022, yayinda kuma za a fara karbar korafe-korafe kan zaben fidda gwanin a ranar 3 ga Fabarairu.
Kudin takardar neman takarar a jam’iyyar ga mai neman takarar kujerar Majalissar Tarayya shine naira miliyan 3.850, yayin da shi kuma mai neman takarar kujerar Majalissar Jiha zai biya naira dubu 850.
‘Yan takarkaru mata da maza masu bukata ta musamman su kuma za su biya kashi 50 cikin 100 na kudin takardun.