For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APC Ta Tabbatar Da Cewar Ita Jam’iyyar Ɓarayi Ce – PDP Kan Shugabancin Ganduje

Jam’iyyar Adawa ta PDP ta kushe jam’iyya mai mulki, APC kan zaɓin tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, inda ta ce dattijon mai shekaru 73 a duniya yana fama da halin cin hanci da rashawa a tare da shi.

A zaman Kwamitin Gudanarwa na APC, wanda aka gudanar jiya Alhamis a Abuja, wanda kuma ya samu halartar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne aka tabbatar da Ganduje da kuma Ajibola Basiru a matsayin shugaba da sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Da take magana kan naɗin Ganduje, jam’iyyar PDP, a jawabin da ya fito daga Sakataren Yaɗa Labaranta, Debo Ologunagba ta ce, APC ta tabbatar da cewa ita kwatamin cin hanci da rashawa ce kuma mafakar ɓarayi, masu cin hanci da sace kuɗin al’umma.

PDP ta ƙara da cewa, daga naɗin Ganduje wanda ƴan Najeriya ke kira da ‘Gandollar’ saboda samun bidiyonsa da ya nuna ƙarara yana cika babbar rigarsa da dalar Amurka wadda aka kawo masa a matsayin cin hanci daga ƴan kwangila lokacin yana gwamnan Jihar Kano, ya tabbatar da cewar APC jam’iyyar cin hanci ce ta maɓarnata da mayaudara.

PDP ta kuma ce, wannan ya nuna rashin niyyar APC ta aiwatar da gaskiya da samar da amana da halin ya kamata da ake buƙata a kan masu riƙe da madafun iko.

PDPn ta kuma tunawa ƴan Najeriya cewa, a watan da ya gabata ne, binciken da Hukumar Karɓar Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta tabbatar da ingancin bidiyon shekarar 2017 na ‘Gandollar’.

Comments
Loading...