Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a yau Asabar ta musanta batun ƴan takarar Shugaban Ƙasa guda goma da suka kasa tsallake tantancewa.
Musantawar dai ta fito ne daga bakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Abdullahi Adamu, lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a babban ofishin jam’iyyar na ƙasa a Abuja.
Rahoton kwamitin tantancewar, wanda John Odigie-Oyegun ya jagoranta, ya kawo ruɗani da rashin tabbas a tsakanin masu neman takarar su su 23, inda kowa yake dakon cikakken sakamakon tantancewar.
Da yake jawabi domin warware yanayin, Abdullahi Adamu ya ce, ƴan takara 13 da akai magana a kansu a matsayin waɗanda suka tsallake sun tsallake ne a matsayin waɗanda suka zo na ɗai ɗai.
“Ina so na baiyana muku ƙarara cewa, babu wani ɗan takara da bai tsallake ba. Abin kamar zaman jarabawa ne. Ko ka ci to akwai matakai daga wanda ya fi ci da kuma wanda ya ci kaɗan.
“Saboda haka babu wani ɗan takara da bai tsallake ba. Shugaban Ƙasa ma ya kirasu cin abinci dare yau gaba ɗayansu,” in ji shi.