Duk da bukatar karin lokaci da kwamitin sasanto na APC karkashin tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Abdullahi Adamu yai domin gabatar cikakken rahoton kammala aikinsa na sasanto, jam’iyyar APC ta cigaba da bin jadawalin Babban Taronta.
A jadawalin kamar yanda TASKAR YANCI ta rawaito a baya ya nuna za a karbi cikakken rahoton sasanto a ranar Talata 1 ga Fabarairu yayinda kuma za a rantsar da tabbatattun shugabannin jihohi a ranar Alhamis ta yau.
To sai dai kuma, rahoton sasanton bai samu kammaluwa ba saboda karuwar korafe-korafe da kuma shari’u na kotu, kamar yanda Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana, inda ya kara da neman karin wa’adi na sati daya, abin da ya jawo ake tunanin jam’iyyar zata canja jadawalin Babban Taronta na kasa dalilin hakan.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, bangarorin jam’iyyar APC na jihohi wadanda ke samun goyon bayan gwamnonin jihar a jihohin da APC ke mulki sune za a rantsar a matsayin shugabannin APC a jihohinsu yau a Abuja.
Bangarorin da zasu rasa damarsu a yau sun hada da bangarorin da ke da goyon bayan Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola; Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo; da kuma na Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed.
Sauran da zasu rasa damar tasu sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, Senator Kabiru Marafa da kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’Aziz Yari’.
An dai samu rikice-rikice da sabani da dama a jihohi masu yawa, wadanda suka samo asali daga rudaddun zabukan shugabannin jihohi da aka gudanar.
A yanzu dai shugabancin APC na kasa ya shirya rantsar da wadanda suke samun goyon bayan gwamnoni a rikice-rikicen in banda a jihar Kano.
A jihar Kano dai har kawo yanzu abun yana duhu, inda aka kasa gane ina APC ta kasa zata goyi baya bayan cin tura da kokarin samar da sasanto a jihar ya yi.
A yanzu hakadai shugabannin jam’iyyar da za a rantsar kusan daga jihohi 30 na Najeriya suna Abuja domin rantsarwar.
Da wakilin PUNCH ya ziyarci babban ofishin jam’iyyar na kasa da ke kan titin Blantyre Street, Wuse 2, Abuja, ya rawaito cewa akwai wadatar jami’an tsaro saboda bayar da kariya idan an samu bore daga wadanda abun baiwa dadiba.