Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da zazzafan martani ga tsagin su Malam Ibrahim Shekarau, biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a kan rushe hukuncin da wata kotu a Abuja ta yi na rushe shugabancin APC a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi ɓangaren Ganduje.
Kadaura24 ta rawaito cewa bayan hukuncin da kotu ta yanke a safiyar wannan rana, Gwamna Ganduje ya ce Banza 7 sun faɗi wan-war akan rashin bin ka’idojin jam’iyya da kuma amincewa da jagorancin sa.
Ganduje Wanda ya yi magana cikin wani faifen video da yake jawabi ga wasu ‘yan majalissu da sauran mukarraban Gwamnatin Jihar Kano, ya godewa Shugaban Riko na Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, bisa kokarin ganin ya sulhunta su da ‘yan G7.
(Kadaura24)