For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

AREWA DA KUDU: PDP Zata Bar Kowa Ya Nemi Takarar Shugaban Kasa

A lokacin da ake tsaka da dakon matsayar jam’iyyu kan yankin da za su mika takarar shugaban kasa a jam’iyyunsu a shekarar 2023, haka kuma a lokacin da kiraye-kiraye sukai yawa kan tabbatar da tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu, jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta ce babu wani dan takarar shugaban kasa da za ta dakatar ko da kuwa daga wanne yanki ya fito a Najeriya.

Jam’iyyar ta ce, za ta bayar da dama ga dukkanin ‘yan takara ba tare da la’akari da jiha ko yankin da mutum ya fito ba.

Wannan ya nuna cewa, ‘yan takarar da ake sa ran iya fitowarsu daga yankin Arewa ko Kudu za su iya fitowa su gwada neman sa’arsu a zaben fidda gwani da jam’iyyar za ta yi a nan gaba.

Kawo yanzu dai, Tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Dr. Bukola Saraki ne kadai ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a duk fadin Najeriya a cikin jam’iyyar PDP.

Saraki wanda dan jihar Kwara ne da ke yankin Arewa ta Tsakiya, ya fito daga yankin Arewa yankin da ake kallonsa a matsayin yankin da mafi yawan masu neman takarar shugaban kasa a PDP za su fito daga shi.

Sauran ‘yan Arewa da ake tunanin za su iya fitowa a PDP sun hada da; Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar; Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido; Gwamnan Bauchi Mai Ci, Bala Mohammed; Gwamnan Sokoto Mai Ci, Aminu Waziri Tambuwal; Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da sauransu.
 
Daga Banagaren Kudu kuma, kawo wannan lokaci, iya Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Anyim Pius Anyim, da kuma Sam Ohuabunwa ne suka nuna sha’awarsu ta nuna yin takarar shugaban kasa a PDP.
 
A tattaunawarsa da jaridar PUNCH, Sakataren Yada Labarai na PDP, Debo Ologunagba ya ce, jam’iyyar ba za ta tsayar da kowa ba da ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara ko saboda shekarunsa ko kuma yankin da ya fito.
 
Ya ce, “Dole ne mu kubutar da kasar daga halin da take ciki a yanzu, kuma akokarinmu na yin haka, bai kamata mu tsaya muna maganar yankin da dan takara zai fito ba, sai dai mu yi maganar, iyawarsa, kwarewarsa da kuma nuna gaskiyarsa wajen aiwatar da aiki.
 
“A PDP, mutane daga kowanne bangare na kasar nan za su samu damar su tsaya takara, abun da kawai zamu tabbatar shine, zaben fidda gwani zai zama na gaskiya da gaskiya babu kunbiya-kunbiya. Bai kamata muna maganar yankuna wajen tantance wanda zai zamewa jam’iyya dan takarar shugaban kasa ba.
 
“Duk wanda ya cancanci ya fito kuma yake da sha’awar yin hakan za a bar shi ya fito. Babu wanda za a hana. Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyya da na kasa su za su zame mana madubi.
 
“Ba za mu hana kowa shiga harkar zabe ba. Idan lokaci ya yi, dukkanin bangarorin jam’iyya za su shiga wajen maganar yanke hukunci kan ka’idojin jam’iyya game da zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa. Wadannan bangarori sun hada da mazabu, kananan hukumomi, shugabancin sassa, ‘yan Majalissar Tarayya, Kwamitin Amintattu, da kuma Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Kasa.”

Comments
Loading...