Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya ce yankinsu na Arewa ta Tsakiya a yanzu ba ya bukatar shugabancin PDP, shugabancin kasa yake bukata a 2023.
Baraje, mai goyawa tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki baya ne kan kudirin da aka hakikance yana da shi na neman shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar da kuma Tsohon Shugaban Majalissar Dattawan dukkansu sun fito ne daga jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
A wata sanarwa da ya fitar wadda DailyTrust ta samu, Kawu Baraje ya ce, duk da cewa jam’iyyar PDP ta tura damar tsayawa takarar shugabancinta zuwa yankin Arewacin Najeriya, hakan ba zai hana yankin Arewa ta Tsakiya shiga neman kujerar shugaban kasa ba.
Ya kuma shawarci PDP da ta rike al’adarta ta adalci, daidaito da gaskiya ta hanyar tabbatar da cewa yankin da bai samu damar fitar da shugabancin jam’iyyar a baya ba an ba shi dama domin fitar da shugaban da zai kai jam’iyyar ga nasara a zabe mai zuwa.
“Tun daga kan Chief Solomon Lar, Chief Audu Ogbeh, Dakta Ahmadu Ali, Chief Barnabas Gemade, da ni kaina, dukkaninmu mun fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiya wanda ya debi lokaci yana jagorantar jam’iyyar tsawon lokaci. Alhaji Bamanga Tukur da Alhaji Adamu Muazu daga yankin Arewa maso Gabas suma sun jagoranci jam’iyyar, sannan Dakta Haliru Bello ya debe shekara daya kacal a matsayin shugaban riko sai kuma Sanata Ahmad Makarfi wanda yai shugabancin riko.”
“Da wannan tarihin, a tsari na gaskiya da samar da dai-daito, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi dacewa da fitar da shugaban jam’iyya na gaba.”
“Mun gano cewa, wadansu shugabanni daga yankin da ba na Arewa ta Tsakiya ba na yin shiri da duk karfinsu domin tunkudo shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Arewa ta Tsakiya da kuma tabbatar da shugabancin bai tsaya a yankinsu ba.
“Idan ma shugaban jam’iyyar ya fito daga Arewa ta Tsakiya, to mu kari ne kawai a wajenmu. ‘Yan takarar shugaban kasa ma za su fito daga yankin domin neman kujerar.
“Ya kamata a sani cewa, matsayarmu a yankin Arewa ta Tsakiya na nan a kan abin da shugabancin jam’iyya ya sanar a baya cewa, tikitin takarar shugabancin kasa zai zama a bude ga duk dan takarar da ya can-canta. Mun yarda cewa, ya kamata jam’iyya ta mutumta batun da ta sanar a bainar jama’a.
“Ba abu ne na tsarin jam’iyyar ba, wadansu su cusa son zuciyarsu kan mutane.”