Jigo a kabilar Yarabawa, Farfesa Banji Akintoye, ya ce Arewa za ta ci gaba da mulki da mamaye Najeriya ba tare da la’akari da wanda ke kan mulki a matsayin Shugaban kasa ba.
Ya yi wannan magana ne daga Jamhuriyar Benin a cikin wata hirar kai tsaye da PUNCH ta yi a Talatar nan.
Akintoye ya yi wannan tsokaci kwanaki bayan Kungiyar Dattawan Arewa ta ce arewa ba za ta yi wasa ba a cikin kasar da a fili yake ta fi kowanne yanki karfin yawan mutane da za a lashe zaben shugaban kasa da su.
Jaridar PUNCH ta ruwaito a baya cewa Daraktan Yada Labarai na Kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum), Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a wani taron da aka yi a Zariya ranar Asabar, yana cewa, “Za mu jagoranci Najeriya kamar yadda muka jagoranci Najeriya a baya kafin mu zama Shugaban kasa ko Mataimakin Shugaban kasa.
Za mu jagoranci Najeriya domin muna da mafi yawan kuri’u, kuma dimokuradiyya ta ce ku zaɓi wanda kuke so.
“Me ya sa za mu yarda da matsayi na baya alhali mun san za mu iya siyan fom da yin takara a ajin farko kuma za mu ci nasara?
“Me ya sa wani ke bukatar ya yi mana barazana da tsoratar da mu? Za mu sami wannan damar amma ku kasance masu tawali’u saboda iko daga Allah yake. Mun gaji shugabanci kuma yin gaskiya ba ya nuni da rashin hankali bane.
“Arewa tana da kima; muna da tawali’u don sanin cewa za mu tafiyar da Najeriya tare da wasu mutane amma ba za mu koma matsayi na biyu ba.
Zai yiwu ba mu da mafi karfin tattalin arziki, amma duk da haka akwai mutanen da ke kokarin daure mu fiye da yadda ake makure mu.”
Yayin da zabukan 2023 ke gabatowa, rashin ingantacciyar siyasa ya yi kamari ga kuma wasu ‘yan Najeriya da yawa ciki har da gwamnonin Kudu 17 da ke neman Shugaban kasa ya fito daga Kudancin Najeriya don maye gurbin mai ci, Muhammadu Buhari, wanda ya fito daga Jihar Katsina, Arewa maso Yammacin Najeriya.
Da yake magana ta cikin shirin PUNCH, Akintoye mai shekaru 86, masani kuma Farfesa na Tarihi, ya ce Arewa ta kasance tana son “mamaye” sauran kasar.
Duk da cewa bai yi magana kai tsaye ba kan maganar kakakin NEF, Akintoye ya ce Najeriya ba kasa ba ce saboda rinjaye na wata kabila akan wasu.
Ya ce, “Ya kai lokaci yanzu da Najeriya za ta kasance ba kasa ba ce. Me yasa na fadi haka? Babu wata kasa a duniya inda sashi daya, yanki daya ke cewa, ‘Za mu ci nasara kan sauran, za mu yi nasara a kan ku, za mu mai da kan mu masu kula da albarkatun kasar ku, za mu fi kula da ku, a mai da ku kasa kamar bayi ‘.”
Akintoye ya ce duk da cewa wasu ‘yan Kudu ciki har da tsoffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun kasance a kan mulki tun bayan dawowar mulkin dimokaradiyya, sun yi aiki karkashin mulkin ‘yan Arewa.
“A karkashin Obasanjo a matsayinsa na shugaban kasa, manyan Arewa sun sa Arewa ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya zuwa kasar Musulunci ta daban. Obasanjo bai iya yin komai a kai ba…
“Ee, Obasanjo Bayerabe ne wanda ake so, muna kaunarsa amma mun san ya yi mulki a cikin wani yanayi lokacin da shugaban Najeriya ke kallon iko a karkashin teburin da sauran mu ba za mu iya yin komai ba. Ba a maganar (Mataimakin Shugaban Kasa Yemi) Osinbajo ba.
“Osinbajo yana daya daga cikin masu ilimi da suka shiga harkokin mulkin Najeriya, ku ga abin da yake yi, shin yana yin su yanda yake so?”
Akintoye, shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin cin gashin kai ta Yarabawa da aka sani da ILANA OMO OODUA, da kuma fitaccen dan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, an gansu tare a taron manema labarai da kuma gangamin.
Lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fara irin wannan aikin a shekarunsa, farfesan ya amsa da cewa, “Ee, ina yin shi ne a karshen shekaruna amma idan ban yi hakan ba, ba na son zuwa kabari da jin cewa kasar da nake so kuma na ba da raina tana mutuwa a gabana kuma na tsaya ban yi komai ba.
“A’a, ina so in iya cewa a raina, na yi gwagwarmaya mai kyau kuma idan muka hadu da Cif (Obafemi) Awolowo, na tabbata zai bude hannayensa kuma ya yi maraba da ni a matsayin da na nagari. Dole ne in yi wannan yanzu.”
Ya kuma tabbatar wa masu tayar da kayar baya na Yarabawa cewa nan ba da jimawa Igboho zai kwato ‘yancinsa daga hukumomin kasar da ke magana da Faransanci.
Igboho, wanda gwamnatin Najeriya ta ayyana a baya ana neman sa, ya kasance a wani gidan yari a Cotonou, Jamhuriyar Benin, tun ranar 19 ga Yuli, 2021 lokacin da aka cafke shi a filin jirgin sama na kasar.
Kalli hira anan: https://web.facebook.com/punchnewspaper/videos/375617334209405