
Gwamnatin Argentina ta sanar da hutun kwana daya a kasar a jiya, don murnar lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafa na FIFA da aka kammala ranar Lahadi a Qatar.
Rahotanni na cewa, a yau da safe ne, ake sa ran tawagar ’yan wasan Argentina za ta isa Buenos Aires, babban birnin kasar, inda shugaban kasar zai tarbe su a yau din, daga bisani kuma gwamnatin kasar za ta shirya musu wani gagarumin bikin taya murna a hukumance.
CRI Hausa