For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ASUU Na Tattaunawa Kan Hukunci Na Karshe Game Da Shiga Yajin Aiki

Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU na fara zaman kwanaki biyu a yau, a Jami’ar Lagos da ke Akoka domin yanke hukunci na karshe game da batun shiga yajin aiki da ya ki ci ya ki cinyewa.

Kungiyar ASUU za ta yanke hukuncin karshe game da batun ta hanyar yin zabe a tsakanin mambobin kungiyar a ranar karshe ta zaman wato gobe Lahadi.

Kungiyar ta nuna damuwarta bisa gazawar Gwamnatin Tarayya game wajen cika wasu alkawuran da akai yarjejeniyarsu tun shekarar 2009.

A ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021 ne kungiyar ASUU ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin sati uku domin ta cika alkawuran da ta dauka.

Malaman Jami’ar sun yi barazanar shiga wani yajin aikin biyo bayan rashin cika alkawarin gwamnatin a wannan lokaci, alkawuran da gwamnatin ta amince da su a baya, amincewar da ta kawo karshen yajin aikin Kungiyar na shekarar 2020.

To amma, bayan zaman Shugabannin Kungiyar a Jami’ar Abuja a ranakun 13 da 14 ga watan Nuwamba na 2021, Shugaban Kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi korafin cewa, duk da zaman da Kungiyar ta yi da Ministan Kwadago, Dr Chris Ngige, a ranar 14 ga watan Oktoba, 2021 kan batutuwan da suka shafi sakin kudade domin gyaran jami’o’in gwamnati, kudaden alawuns na koyarwa, tsarin karbar albashi na UTAS, biyan bashin kudaden arrears na ciyarwa gaba, sake kulla yarjejeniyar 2009 tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, da matsalolin tsarin biyan albashi na IPPIS, babu ko daya daga bukatun kungiyar da aka cika.

Bayan baiyanar barazanar kungiyar, Karamin Ministan Kwadago, Emeka Nwajiuba, ya yiwa kungiyar alkawarin cewa za a cika alkawuran.

‘Yan makonni bayan wannan, ASUU ta fasa shiga yajin aikin da ta shirya shiga a lokacin da Gwamnatin Tarayya ta biya naira biliyan 22.1 na alawuns din koyarwa ga masu koyarwa a jami’o’in Gwamnatin Tarayya.

(PUNCH)

Comments
Loading...