Kungiyar Malaman Jami’oi reshen Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a Jihar Jigawa ta zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin ingiza kungiyar shiga yajin aiki.
Kungiyar ta baiyana hakan ne a takaradar da ta rabawa manema labarai wadda Shugaban ASUU reshen SLU Kafin Hausa, Dr. Mustapha Hussaini ya sanyawa hannu.
A cikin takardar, kungiyar ta baiyana kokarin gwamnati na kakabawa ‘ya’yanta shiga tsarin biyan albashi na IPPIS, yawaitar jami’o’in jihohi, mutumta yarjejeniyar 2020, da kin kulawa da halin da jami’o’i ke ciki a matsayin takalar rigimar da za ta kai kungiyar ga tsunduma yajin aiki.
Kungiyar ta ce, a lokacin da masu rike da madafun iko ba sa tura ‘ya’yansu makarantun firamare da sikandare na gwamnati, sun kuma tabbatar da cewa wadannan makarantu ba su kai matsayin wadanda ‘ya’yansu ke halarta ba.
ASUUn ta kuma yi zargin cewa, bayan cimma wancan kudiri na su, masu rike da madafun ikon sun sako jami’o’i a gaba.
Kungiyar ta ce, ya kamata ‘yan kasa su lura da yanda suke daukar hotuna da ‘ya’yansu a makarantun kasashen waje kamar su Amurka da Birtaniya, sun kyale makarantun cikin gida.
A baya dai, kungiyar reshen Jami’ar Sule Lamido ta yi biyayya ga uwar kungiyar ta kasa, inda ta aiyana ranar 8 ga wannan watan a matsayin ranar da ba za ai karatu ba, saboda a fadakar da ‘yan kasa kan irin halin shakulatun bangaro da gwamnati take yi da yarjejeniyar da aka kulla.