For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ASUU Ta Baiyana Farfesancin Pantami A Matsayin Wanda Ya Saba Ka’ida

Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta kushe ciyarwa gaban da akaiwa Ministan Sadarwar Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami zuwa matakin Farfesa.

Kungiyar ta baiyana hakan ne bayan kammala zaman tattaunawa ta da ta yi, inda ta baiyna lamarin da “abin da ya saba ka’ida”.

Wannan magana ta fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, a yau Litinin.

Ya ce, “Ba zai taba yiwuwa ka zama minista kuma malami a jami’a a lokaci guda ba. Wannan daurewa karya gindi ne.

“Ya kamata Pantami ya ajjiye aikinsa na minista domin a tuhumeshi da yin aiki biyu a karkashin gwamnatin tarayya daya. Bai cancanta ba. Pantami bai kamata a ce masa farfesa ba.”

A watan Satumba na shekarar 2021 ne, hukumar Federal University of Technology, Owerri, FUTO ta daga Pantami da wasu mutane bakwai zuwa matakin farfesa a zaman makarantar na 186.

Daukaka ministan ya jawo cece-ku-ce, inda da yawa suka kushe matakin da FUTO ta dauka na ciyar da ministan gaba, wanda ba malami ba ne a jami’a, wanda kafin zamansa minista malamin jami’a ne daga baya kuma ya shiga siyasa.

“Mun yanke shawarar tuhumar mambobin ASUU da suka shiga maganar kara masa girman hadi da VC na FUTO,” in ji shi.

Comments
Loading...