Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU wadda ke cikin yajin aiki ta ce, tana jiran jin ta bakin Gwamnatin Tarayya kan bukatunta.
Kwamitin sasanto da sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs ya gana da ASUU a ranar Litinin da ta gabata, a ƙoƙarinsa na sake duba yarjejeniyar.
An yi wannan zaman ne da sauran ƙungiyoyin da suka shafi jami’o’i waɗanda su ma suna cikin yajin aiki a halin yanzu.
Shugaban Ƙungiyar ASUU, Emmanuel Osodeke, ya faɗawa wakin PUNCH cewa, tattaunawar ta yi daɗi, inda ya ce, suna tsammanin gwamnati zata magantu kan matsayar da ƙungiyar ta cimma da ƴan kwamitin.
Lokacin da aka tambayeshi ko ASUU zata janye yajin aikin da take yi kwanan nan tun da tattaunawa ta yi daɗi da ƴan kwamitin, Osodeke ya ce, “Ban sani ba ko zamu janye yajin aiki kwanan nan. Muna dai jiran hukuncin gwamnati na ƙarshe kan lamarin.
“Kwamiti ne na hukumomin gwamnati daban-daban. Akwai buƙatar su koma wajen shugabanninsu su duba abin da muka amince a kai sannan su waiwaice mu. Idan har sun waiwaice mu to zamu ba ku cikakken bayani.”
Osodeke ya kuma bayyana cewa tsarin biyan albashin da ASUU ta gabatar na University Transparency and Accountability Solution, UTAS na cikin tsarin tantancewa a hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani ta NITDA.
Ƙungiyar ASUU dai ta fara yajin aiki ne tun a ranar 14 ga watan Fabarairu na wannan shekarar bayan gazawar Gwamnatin Tarayya na cika alƙawuran da ke tsakaninsu.