Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, da Gwamnatin Tarayyar Najeriya sun cinma matsaya bayan samun shiga tsakanin da Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila.
An samu daidaiton ne a zaman sasanton da aka gudanar a Majalissar Tarayya yau Alhamis.
Kakakin Majalissar ya gayyaci Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, Ministar Kudi, Zainab Ahmed da kuma shugabancin ASUU zuwa wajen tattaunawar domin magance yunkurin shiga yajin aiki.
A wajen tattaunawar, an samu matsaya kan dukkan alkawuran da aka samu tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya tun shekarar 2009.
A jawabinsa, Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce, Majalissar Wakilai ba za ta zauna tana kallon abubuwa na lalacewa saboda sabanin fahimta tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya ba.
Gbajabiamila ya ce, ‘yan Najeriya ba su iya jure yajin aiki ba, haka kuma ba za su zama makamin kungiyar ASUU ba wajen tura bukatunsu a ko da yaushe.
Ya bayyana cewa, dukkan bangarorin dole su karbi laifin abin da ke faruwa.
Ya kuma kara da cewa, kungiyar ASUU ta yi matukar hakuri, saboda haka dole ne gwamnati ta yi kokari wajen cika na ta bangaren na yarjejjeniyar.
Da yake magana a wajen tattaunawar, Shugaban Kungiyar ASUU, Prof. Victor Emmanuel, ya ce, akwai batutuwa da dama da yarjejjeniyoyi da gwamnati tai watsi da su..
Ya ce gwamnati a lokuta da dama ta kasa magance manyan matsalolin kamar biyan alawuns-alawuns, gudanar da manyan aiyuka, UTASS da sauransu wadanda ya ce sune suke tunzura ‘yan kungiyar shiga yajin aiki.
Ya ce sun sami amincewa tsakaninsu da gwamnati kan Naira Tiriliyan 1.3 da kungiyar ta bukata domin magance matsalar manyan aiyuka da sauran aiyuka a baya.
Ya bayyana cewa, an amince da cewa, za a na fitar da kudaden kashi-kashi da Naira Biliyan 200 a karon farko wadda har yanzu ba a fitar ba.
Ya ce daga baya an rage kudaden zuwa Naira Biliyan 52.127, inda za a ware daga ciki Naira Biliyan 30 domin aiyukan gine-gine da kuma Naira Biliyan 22.127 domin alawuns na EAA wadanda duk ciki babu wanda gwamnatin tarayya ta yi.
A nasa bangaren, Karamin Ministan Ilimi, Henry Nwajuba, ya ce duk kanin korafe-korafen ASUU gaskiya ne kuma gwamnati na kan kokarin ganin an cimma wadan nan bukatu, musamman alawuns na EAA da kuma kudaden aiwatar da aiyuka a jami’o’in.
Da take na ta jawabin, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce, akwai tanadin da akai domin biyan kudaden, kuma ma wasu daga cikin kudaden sun samu, za a fara biyan a cikin sati.
Bayan bayanan Ministocin biyu, shugabancin Kungiyar ASUU ya amince da bayanan, inda ya bayyana cewa za su lura da cigaban da aka samu kafin karewar wa’adin da suka bayar na shiga yajin aiki.
Labari: DailyTrust
Fassara: Kabiru Zubairu