For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ASUU Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani A Jihar Taraba

Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU, reshen Jami’ar Jihar Taraba ta sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Wannan ya biyo bayan amincewar da kungiyar ta samu daga uwar kungiyar ASUU ta kasa na shiga yajin aikin domin neman hakkokinsu a wajen gwamnatin jihar da take cewa babu ma’aikacin da ke bin ta albashi.

Da take tashi daga zaman tattaunawa na mambobin kungiyar, kungiyar ta jaddada cewa, dalilin shiga wannan yajin aikin ya samo asali ne daga gazawar gwamnati na biyan alawuns din koyarwa, bashin albashin karin girma, da rashin daidaito a biyan malamai a albashi da kuma rashin takamaimai matsaya kan tsarin kudaden fansho da ladan kammala aiki.

KU KARANTA WANNAN: An Kama Malamin Jami’a Saboda Bukatar Yin Lalata Da Karbar Kudi A Wajen Daliba Don Ba Ta Maki

Mr Samuel Shitaa, wanda shine Shugaban Kungiyar ASUU a Jami’ar Jihar Taraban ya bayyana cewa, sauran dalilan shiuga yajin aikin sun hada da rashin aiwatar da yarjejjeniyoyin da akai da kuma rashin kewaye jami’ar da katanga.

Da take mayar da martani kan matakin shiga yajin aikin, gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Manyan Makarantu, Edward Baraya, ta bayyana cewa kungiyar ba ta tuntubi gwamnatin jihar ba kafin yanke hukuncin.

Ya bayyana mamakinsa kan cewa, me yasa kungiyar ASUU zata dau wannan mataki bayan gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen ganin magance matsalolin kafin karshen wa’adinta.

Haka shima mai baiwa gwamna shawara a kan kafafen yada labarai da hulda da jam’a, Bala Dan-Abu, ya bayyana a zantawarsa da manema labarai cewa, babu ma’aikacin da yake bin gwamna mai barin gado a jihar albashi.

Comments
Loading...