Biyo bayan rashin biyan malaman jami’o’in gwamnatin tarayya cikakken albashin watan Octoba, reshen jami’ar Jos na Ƙungiyar ASUU ya umarci mambobinta da su zauna a gida har sai gwamnati ta biya su albashinsu da ta riƙe.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shugaban ASUU a jami’ar, Dr Lazarus Maigoro, yana faɗar haka a garin na Jos a jiya Juma’a.
Sai dai kuma Maigoro ya ce ba yajin aiki suka koma ba, amma dai an ɗauki matakin ne bayan taron da suka gudanar a ranar Juma’ar sakamakon ƙin biyan su cikakken albashin da gwamnati ta yi.
Shugaban ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ɓangarorin yarjejeniyar da suka cimma da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabeamila shi ne, gwamnati za ta biya kashi 50 cikin 100 na albashin watanni 8 da ta riƙe musu da zarar sun janye yajin aiki.
“Yanzu da muke magana, albashin kwana 17 kawai aka biya mu na watan Oktoba daga ofishin akanta janar na ƙasa,” a cewarsa.