For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ASUU Za Ta Baiyana Matsayarta A Yau Litinin Kan Tsunduma Yajin Aiki

Ana tsammanin Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, za ta baiyana matsayarta a yau Litinin kan ko za ta tsunduma yajin aiki.

Mambobin Kwamitin Zartarwar Kungiyar sun yi ta tattaunawa kan wannan batu tun ranar Asabar.

Mambobin Kwamitin da suka hada da jagororin kungiyar a reshen Jami’oi, suna yin zaman nasu ne Jami’ar Lagos da ke Akoka kuma za su karkare zaman a yau.

Sun yi alkawarin cewa, za su yiwa manema labarai bayanin halin da ake ciki bayan kammala zaman na tsawon kwanaki biyu a yau Litinin.

Akwai damuwa a zukatan dalibai da iyayen dalibai kan fargabar ko ASUUn za ta tsunduma wani sabon yajin aikin.

ASUU ta yanke shawarar aiwatar da zaman tattaunawar ne bayan ta wayar da kan malamai, dalibai da iyayen dalibai kan abubuwan da za su sa ta iya tsunduma yajin aiki.

Ana tsaka da wannan wayar da kan ne a jami’o’i, Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar III da Shugaban Kungiyar Kiristoci, CAN, Dr Samson Ayokunle; suka ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan gazawar gwamnati na cika alkawuran da ke yarjejeniyar shekarar 2009 wadda gwamnati da ASUU suka sanyawa hannu.

To sai dai kuma, Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Oshodeke, da sauran shugabannin kungiyar daga jami’o’i sun baiyana cewa Gwamnatin Tarayya ba abar yarda ba ce, biyo bayan cigaba da kin aiwatar da yarjejeniyar da ta sanyawa hannu ita kungiyar, wadda ta jawo aka dakatar da yajin aikin shekarar 2020.

Comments
Loading...