For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

ASUU Za Ta Shiga Yajin Aikin Gargadi Na Wata 1

Bayan tattaunawa mai tsayi wadda Ƙungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta yi tun daga ranar Asabar kawo safiyar Litinin din nan, shugabancin kungiyar ya amince da shiga yajin aikin gargadi na wata daya domin sanya gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Wata majiya da ta bukaci a boye sunanta, ta baiyanawa jaridar VANGUARD cewa, za a shiga yajin aikin gargadin ne domin a baiwa gwamnati dama ta yi abin da ya dace, idan kuma ta kasa a tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

“Muna son mu baiwa gwamnati dama ne, domin ta gane ta kuma kare gurguntar ilimin jami’o’in kasar. Muma iyayen yara ne kuma muna da ‘ya’ya a jami’o’in, amma ba za mu bari muna gani tsarin neman ilimi ya durkushe a kasar ba.

“Fafutukarmu bukatar kowa ce kuma idan an daidaita tsarin za mu ji dadi. Manyan mutane a kasar nan sun shiga lamarin, amma kamar gwamnati ba ta damu ba. Shugabanmu na kasa zai yi cikakken bayani lokacin da zai yiwa manema labarai jawabi idan an jima a yau,” in ji majiyar.

(VANGUARD)

Comments
Loading...