Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a yau Litinin, ya hadu da Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike a Abuja.
Atiku dai ya kayar da Wike ne a zaben fidda gwani na masu neman takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP wanda aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata a Abuja.
Ganawar ta yau Litinin, an baiyana cewa an yi ta ne domin a sasanta bangarorin guda biyu tare da karawa PDP karfin lashe zaben shekarar 2023.
Ganawar ta samu halartar tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma wanda ya nemi takarar Shugaban Kasa a PDP, Ayodele Fayose tare da sauran manyan jam’iyyar ta PDP.
Cikakken bayani kan ganawar ba ta baiyana karara ba a dai-dai lokacin rubuta wannan labarin, sai dai kuma wakilin PUNCH ya gano cewa, Atiku na kokarin neman abokin takara ne a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa wanda zai fito da Kudancin Najeriya.