For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Atiku Abubakar Ya Lashe Tikitin Yi Wa PDP Takarar Shugaban Ƙasa A 2023

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a lokuta daban-daban, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen fidda gwani na Shugaban Ƙasa a babbar jam’iyyar adawa, Peoples Democratic Party, PDP.

An baiyana Atiku a matsayin wanda yai nasara a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a Abuja ne, bayan ya samu ƙuri’u 371.

Ya samu nasara a kan Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya samu ƙuri’u 237.

Sauran ƴan takarar da suka samu ƙuri’u a zaɓen sun haɗa da Sanata Bukola Saraki wanda ya sami ƙuri’u 70; Sai Sam Ohuanbunwa wanda ya sami ƙuri’a 1; Sai Anyim Pius Anyim da ya sami ƙuri’u 38; Sai Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya sami ƙuri’u 20.

Tun gabanin fara zaɓen ne dai aka rawaito cewa, Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga neman takarar ya kuma mika goyon bayansa ga Atiku.

Atiku Abubakar dai ya daɗe yana neman takarar Shugaban Ƙasa a Najeriya.

A shekarar 1993 ya nemi jam’iyyar Social Democratic Party, SDP da ta tsayar da shi a matsayin mai yi mata takarar Shugaban Ƙasa, amma Moshood Abiola da Baba Gana Kingibe suka kayar da shi.

A shekarar 2007 Atiku ne ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Action Congress, AC, inda ya samu nasarar zuwa na uku bayan Umaru Musa Ƴar’adua na PDP da Muhammad Buhari na ANPP.

A shekarar 2011, Atiku ya tsaya karar neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi ɗan takarar Shugaban Ƙasa, inda Shugaban Ƙasa mai ci a lokacin, Goodluck Jonathan ya kayar da shi.

A shekarar 2014, ya shiga jam’iyyar All Progressives Congress, APC gabanin zaɓen shekarar 2015 ya kuma tsaya takara a zaɓen fidda gwani na Shugaban Ƙasa inda Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

A shekarar 2017, Atiku Abubakar ya koma jam’iyyar PDP kuma ya samu damar yi mata takara a zaɓen shekarar 2019 sai dai kuma Muhammadu Buhari na APC ya ƙara kayar da shi.

Comments
Loading...