Daga: Abu Hammad
Kamfanin jirgin saman Azman ya dakatar da tashi da sauƙa a jihar Kaduna, kwanaki kadan bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma’aikata.
Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai dakatar da zirga-zirga a Kaduna daga ranar Litinin 28 ga watan Maris da ta wuce.
Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne saboda yanayi na tsaro a filin jirgin saman.
Matakin kamfanin dai ya sa matafiya sun yi cirko-cirko a filin jirgin saman na Kaduna saboda ƙarancin jiragen da za su kai su inda za su je.
Hukumar gudanarwar kamfanin ta sanar da cewa za a dakatar da zirga-zirgar ne na zuwa wani lokaci, ma’ana kafin yanayin tsaro ya inganta a filin jirgin saman na Kaduna.