Malamin Addinin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya ce, Takarar Musulmi da Musulmi da Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba dole ba ne, saboda hakan ba shi da wata alaka da addini.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da siyasar addini da bangaranci saboda duk bangarorin suna da abubuwan da suka shafe su.
Sheikh Gumi ya yi wannan bayani lokacin da ‘yanjarida ke yi masa tambayoyi a gidansa da ke Kaduna kan babban zabe mai zuwa.
Gumi da yake amsa tambayar da akai masa kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu wanda ke ikirarin cewa yanzu lokacinsa ne na zama shugaban Najeriya, Malamin ya ce Tinubu kwararren shugaba ne.
“Bai dace gareshi ba ya ce juyinsa ne. Babu wani abun cewa lokaci na ne. Kar ka ce lokaci na ne.
“Kwararren shugaba ne, zai iya. Dan takara Musulmi mataimaki Musulmi ba dole ba ne. Duk mun sani. Duk ‘yan siyasar nan neman kuri’u suke. Dan takara Musulmi mataimaki Musulmi ba don addini aka yi ba.
“Ko zai bayar da nasara ko ba zai bayar ba, bana so na yi hasashe a kai, amma dai akwai matsaloli da yawa a kai. Tabbas duk jam’iyyu suna da matsalolinsu. Takarar Musulmi da Musulmi zai zama wani gwaji wanda wasu zasu koya a gaba ko su yi watsi da shi,” in ji shi.
A kan Peter Obi kuma, Gumi ya ce, akwai bukatar ya hada kai da sauran bangarorin Najeriya, inda ya kara da cewa akwai bukatar ya zama yana ko ina, ba wai barin siyasarsa a yanki daya ba.