Baindiye na farko, Rishi Sunak zai zama firaministan birtaniya a yau Talata bayan ya gana da Sarki Charles.
A yau din ne kuma Rishi Sunak zai yi jawabi a wajen gini mai lamba 10 da misalin karfe 10:15 na safe kafin daga bisani ya tafi Fadar ta Bucking-ham.
A Fadar, Sarkin zai gana da sabon shugaban jam’iyyar Conservative, wanda shine Firaminista na uku a cikin kasa da watanni uku – inda za a bukace shi da kafa sabuwar gwamnati.
Sunak shine kuma Firaminista na biyu da sarkin zai nada tun bayan darewarsa karagar mulki biyo bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth a watan Satumba.
Bayan ganawar, Sunak zai dawo Downing Street inda zai kara gabatar da wani jawabin da misalin karfe 11:35 na safe.
An dai sanar da cewa, Sunak ya lashe zaben zama shugaban jam’iyyarsa ta Conservative a jiya Litinin da rana, yayin da aka rawaito cewa, Sarki Carles ya yi tafiya zuwa London kamar yanda aka tsara tun a baya.