For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ba Mu Yanke Hukunci Kan Yankin Da Dan Takarar Shugaban Kasa Zai Fito Ba – PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta sanar da cewa, ta samu labari ana yada cewa ta yanke matsayar yankin da ɗan takarar Shugaban Ƙasa zai fito a jam’iyyar a zaben shekarar badi ta 2023.

Sakataren Yada Labarai na PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Asabar.

Sanarwar ta ce, “kwata-Kwata babu wannan maganar, jam’iyyarmu ba ta ma san da wannan zancen ba.

“Domin kaucewa kokonto, PDP tana mai jaddada cewa har yanzu ba ta fidda matsaya a kan yankin da ɗan takarar Shugaban Ƙasa zai fito ba.

“PDP jam’iyya ce da take bin tafarkin dimukuraɗiyya don haka duk wani hukunci da za mu yanke muna bin sa bisa tsari, kuma game da yankin da dan takara zai fito, muna kan tuntuɓa, tattaunawa da duba yanayi da halin da ƙasar nan take ciki wanda suka haɗa da samar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma samar da cigaban ƙasar nan.”

KU KARANTA: ‘Yan Najeriya Ba Sa Bukatar Magajinka Daga Bakinka – PDP Ga Buhari

Jam’iyyar PDP dai ta yi kaurin suna wajen maganar ware bangaren da dan tankara zai fito tun zamanin Obasanjo, duk da kasancewar lokaci daya ne wannan kudiri ya tabbata yayin da Obasanjo dan Kudu ya mika mulki ga ‘Yar’adua wanda dan Arewa ne.

Sanarwar ta PDP ta kara da cewa, “PDP tana kira ga dukkan ƴan Najeriya, da kuma dukkan magoya bayanmu da su yi watsi da wannan maganar da ba ta da tushe balle makama. Jam’iyyar tana kira ga waɗanda suka yi wannan maganar da su janye ta.”

Comments
Loading...