Kungiyar Dattawan Arewa t ace yankin Arewa zai bi cancanta ne a zaben Shugaban Kasa ba tare da la’akari da yankin da dantakara ya fito ba a shekarar 2023.
Kungiyar ta ba da tabbacin cewa ba za ta kara maimaita kuskuren da tai ba kamar yanda tai ga Shugaba Buhari a zaben 2015.
Kungiyar ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin da na sani, ba kadai ga Arewa ba har ma da Najeriya gaba daya.
Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na kungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da ‘yan jaridu, a wani bangare na taron jagororin Arewa wanda aka gabatar a Arewa House, Kaduna a yau Asabar.
KU KARANTA: Iya Iyawar Buhari Kenan, Ba Zai Iya Kara Komai Ba – Obasanjo
Daraktan ya kuma ce dan Arewa da dan’uwansa dan Kudu suna da ‘yanci na neman kujerar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2023.
Ya kuma kara da cewa, yankin Arewa zai zabi Shugaban Kasa wanda ya cancanta ne a 2023, ba tare da la’akari da cewa daga Kudu ko Arewa yake ba.
Baba Ahmad, ya tabbatar da cewa, babu wani dan takarar Shugaban Kasa daga Arewa da za a yarda yayi amfani da yankin a zaben 2023, inda ya kara da cewa irin kuskuren da yankin yayi kenan a zabar Buhari.
Ya kuma ce an yaudari yankin Arewa ne wajen yarda da Buhari, inda aka yi tunanin Kasa za ta gyaru, sai dai kuma abin da aka gani ya saba da abin da aka yi tunani a kan Shugaba Buharin.