
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya rubutawa Majalisar wakilan kasar wasika, inda a ciki ya yi bayanin dalilin da ya sa ba zai amsa goron gayyatar da suka aika ma sa ba.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ne ya karanta wasikar ta Emefiele, a zauren majalisar a jiya Talata.
Jaridar Premium Times, ta ambato Gbajabiamila yana shaidawa zauren majalisar cewa Emefiele, zai tafi kasar wajen ne domin duba lafiyarsa don haka ba zai samu damar halartar zaman ba.
Kakakin majalisar wakilan ya ci gaba da cewa: ”Idan ba a manta ba majalisar ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriyar ya bayyana gabanta a ranar Alhamis din makon da ya wuce, amma bai samu zuwa ba saboda ya na tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke halartar taron kasashen Afirka da Amurka a birnin DC.”
Gwamnan CBN na shan matsin lamba tun bayan kaddamar da sabbin takardun naira 200, 500 da 1000 da aka yi, wasu na ganin baidace ba saboda kudin an yi su kodaddu da ake fargabar masu damfara ka iya yin irinsu, amma CBN ya ce sam lamarin ba haka ya ke ba.