Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya mayar da martani kan maganar yiwuwar komawarsa jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
El-Rufa’i dai na mayar da martani ne kan iƙirarin da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023, David Bwala ya yi na cewar kwanannan tsohon ministan Abujan zai fice daga APC.
A shafinsa na Twitter, Bwala, wanda kwanannan ya fice daga APC, ya ce, yana da tabbacin cewa, El-Rufa’i zai shiga jam’iyyar PDP kafin zaɓen 2023.
Ya kuma bayyana Gwamnan Kadunan a matsayin ɗaya daga cikin kyawawan ƴan siyasar da yankin Arewa ya samar.
Sai dai kuma, da yake mayar da martani a shafinsa na Twitter, El-Rufa’i ya ce, “Na gode @BwalaDaniel amma ba haka ba. Har abada, kai ko gawata ba za a samu a cikin sabuwar jam’iyyar da ka shiga ba. Ni har yanzu dariya nake yi!!! – @elrufai”.