Ƴan takarar neman shugabancin jam’iyyar APC shida sun janye takararsu tare da zaɓar abokin takararsu, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin ɗan takarar maslaha.
Sanata Adamu dai shine wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zaɓa a matsayin wanda zai shugabanci jam’iyyar APC a matakin kasa.
Ƴan takarar dai sun baiyana matakin nasu ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan jiya Juma’a, wadda kuma TASKAR YANCI ta samu.
Wasikar dai an tura ta zuwa ga Shugaban Karamin Kwamitin Zaɓen APC, sannan kuma Sanata George Akume ne ya sanya mata hannu.
Wasiƙar ta ce, “Cikin girmamawa ina la’akari da kiran da Shugaban Kasa ya yi ga ƴan takarar shugabancin babbar jam’iyyarmu domin su yarda da ɗan takarar maslaha, inda aka amince da Abdullahi Adamu a matsayin ɗan takarar maslaha na shugabancin jam’iyya, muna miƙa takardar janyewarmu mu da za a zaiyano a ƙasa:
1. H.E Sen. Tanko Al-Makura 2. H.E Sen. George Akume
3. H.E Abdulaziz Yari
4. Sen. Sani Musa Muhammed
5. Comm. Etsu Muhammed 6. Turaki Saliu Mustapha.”
