For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BABBAN TARON APC: An Kama Ƴan Sane A Eagle Square

Jami’an tsaro sun cafke mutane 3 da ake zargi da yin sane a filin da jam’iyyar APC ke gudanar da babban zaben shugabanninta na kasa a Abuja.

An kama mutanen ne lokacin da suke sace wayoyin mutane a kofar shiga filin taron.

Wani jami’in tsaro da ba ya buƙatar a baiyana sunansa, ya baiyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a yau Asabar cewa, waɗanda ake zargin sun yi amfani ne da turmutsitsin mutane a ƙofar shiga filin taron na Eagle Square inda suke sace wayoyin mutane.

“Mutum uku daga cikinsu suna aiki ne tare, suna sace wayoyin mutane da kuma kuɗaɗe.

“Sun yi amfani da gaggawar da wakilai (delegates) ke yi wajen shiga filin domin su sace musu wayoyi da kuma kuɗaɗe.

“Abun da ya faru shine, ba su san mun sanya ƴan sandan leƙen asiri a ƙofar shigar, suna lura da yanda wakilan ke shiga filin taron ba.

“Wannan ne abun da ya faru, jami’inmu ya kama su suna kan aikinsu bayan sun sacewa wasu wayoyinsu,” in ji jami’in.

Jami’in tsaron ya kuma ce, za a kai waɗanda ake zargin zuwa babban ofishin ƴansanda domin ci gaba da bincike.

(NAN)

Comments
Loading...